Wata yarinya Da Bata Wuce shekara 10 Ba Ta Tashi Kanta Da Bam A Borno 



Wata karamar yarinya da ake jin ‘yar shekara 10 ce ta tarwatsa kanta a yayin da ta tunkari wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Banki a jihar Borno, lokacin da sojoji suka tare ta.
Sojojin sun nemi ta daga hijabinta sama, inda suka ga abubuwan fashewa da ta daura a kugunta. Daga nan sai ta ja kunamar bam din ya tashi.
Kungiyar Boko Haram tana amfani da kananan yara da matasa, inda take sanya su kai harin kunar-bakin-wake a masallatai da kasuwanni.
A baya-bayan nan ma hedikwatar tsaron Nijeriya ta yi gargadi kan yadda ake amfani da mata dauke da goyon jarirai wajen kai harin kunar-bakin-wake yankunan a arewa maso gabashin kasar nan.

You may also like