Watakila APC ta gudanar da babban taronta birnin Legas


Akwai yiwuwar jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da babban taron zaben shugabanninta, a birnin Legas.

Wasu majiyoyi dake cikin jam’iyar sun fadawa jaridar Daily Trust cewa babban taron zai gudana a birnin Lagos duk da adawar da hakan ke fuskanta daga wasu manyan masu ruwa da tsaki dake jam’iyar wadanda ke fargabar cewa baza a kare musu bukatunsu ba matukar aka yi taron a birnin Legas.

“Birnin Lagos ne zai kasance wurin babban taron duk da shakku da kuma fargaba da wasu yan jam’iyar ke nunawa.Wadanda za su kawo tanagarda ana lura da su,” a cewar majiyar.

Ranar Lahadin da ta gabata ne jam’iyar ta fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin gudanar da zaben su 68 karkashin shugabancin gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar.

Babban taron zai gudana ranar 14 ga watan Mayu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like