Watakila Haaland ba zai buga wasa da Arsenal ba – GuardiolaErling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Laraba Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester City a kwantan wasan Premier League karawar mako na 12.

Arsenal mai maki 51 tana ta daya a kan teburi da tazarar uku tsakaninta da City ta biyu mai 48.

Sai dai watakila Erling Haaland ba zai buga wasan ba, bayan da ya ji rauni a fafatawar da City ta doke Aston Villa 3-1 a Etihad ranar Lahadi a Premier League.

Haaland wanda ya ci kwallo 25 a babbar gasar tamaula ta Ingila a bana, an sauya shi a wasan Lahadin lokacin da City ke cin 3-0.Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like