
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya ce watakila raunin Marcus Rashford ya yi muni a wasan da suka doke Everton 2-0 ranar Asabar.
Mai shekara 25 da kwallon tawagar Ingila, ya ji rauni a Old Trafford a wasan mako na 30 a Premier League daf da za a tashi wasan.
An nuna wani faifan bidiyon Rashford, wanda yake tafiya da kyar da dingishi zuwa dakin hutun ‘yan wasa.
An cewa Ten Hag raunin Rashford ya yi muni a lokacin tattaunawa da ‘yan jarida, sai ya amsa da tamabayar ”Ko kai likita ne?”
Sai dai kociyan ya bayyana damuwa kan yadda United ke buga wasannin da yawa, wadda ta ci Brentford 1-0 ranar Laraba, sai kuma ta yi wasa da tsakar ranar Asabar.
Ranar Alhamis United United za ta buga wasan farko a daf da karshe zagayen quarter finals a Europa League da Sevilla a Old Trafford.
”Bari mu jira likitoci su auna koshin lafiyarsa, daga nan za mu tantance abin da ya kamata mu yi.”
Nasarar da United ta samu a kan Everton ya sa ta ci gaba da zama ta hudu a teburin Premier League.
Ten Hag ya fada cewar tun farko ya so ya canja Rashford, to amma United za ta kara da Sevilla, yana fatan hada Rashford da Anthony Martial, shi ya sa bai sauya shi ba.
Everton wadda ta yi rashin nasara da ci 2-0 a Old Trafford ta koma ta 17 a kasan teburi da maki 27.