Watakila Southampton ta bai wa Marsch aikin horar da itaJesse Marsch

Asalin hoton, Getty Images

Southampton na sha’awar bai wa Jesse Marsch aikin kociyanta, domin maye gurbin Nathan Jones.

Kwana takwas da Leeds United ta kori Marsch, wanda yake tattaunawa da kungiyar St Mary, domin cimma matsaya a yanzu haka.

Ranar Lahadi Southampton ta sallami Jones daga aiki, bayan da Wolves ta doke ta 1-0 da hakan ya sa ta zama a karshen teburin Premier.

Kungiyar St Mary za ta ziyarci Chelsea ranar Asabar a gasar Premier, sannan ta kara da Leeds a makon gaba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like