An watsa wa Obama kasa a ido


 

Barcin ‘ya ‘yan Masarautar kasar Saudiyya ya katse tun bayan watsa kasa a idon Barack Obama da ‘yan majalisar dattawan Amurka suka yi,wanda hakan zai bada damar gurfanar Saudiyawa gaban kotu game da batun hare-haren ta’addanci na ranar 11 ga watan Satumban 2001.

Kusan illahirin ‘yan majalisar ne suka yi watsi da hawa kujerar naki da Barack Obama ya yi domin kare Amurka da Saudiyya daga duk wata barazana.

A ranar Alhamis din nan ce,shugabannin diflomasiyyar Saudiyya suka sanar wa da Amurka cewa,wannan mummunar mataki da ta dauka zai iya zama silar lalacewar huldar kud da kud da suka kullo tun shekaru aru-aru da suka gabata.

Saudiyyawa dai na ci gaba da karyata zargin da aka yi musu ,inda a shekarar 2004 wani kwamitin bincike na kasar Amurka ya wanke su daga duk wani zargi.

Amma tuni Amurkawa da dama suka dasa ayar tambaya,inda suka ce idan Saudiyya bata da hannu a hare-haren 11 ga watan Satumba, to me yasa ake ci gaba da cewa 15 daga cikin ‘yan ta’adda 19 wadanda suka kashe kusan Amurkawa dubu 3,’yan kasar Saudiyya ne ?

You may also like