Wayar Nokia 3310 Ta Dawo Kasuwa Bayan Shekaru 17Kamfanin kera wayoyin zamani na Nokia ya sake kaddamar da wayar nan mai ‘karko wadda ta karbu ga jama’a a shekarun baya sanfurin Nokia 3310.
Ita dai Nokia 3310 an fitar da ita ne tun a shekarar 2000, wato tun farkon fitowar wayoyin zamani, an dai san wayar da rike caji da kuma ‘karko kasancewar duk faduwar da za tayi ba ta fashewa.
An dai kaddamar da wayar ne a babban taron Mobile World Congress da aka gudanar ranar Lahadi a Barcelona, wadda da zarar wanda ya san wayar a baya zai iya gane ta cikin gaggawa, duk kuwa da kwaskwarimar da akayi mata.
Ita dai sabuwar Nokia 3310 an kera ta ne yadda zata kai kwanaki talatin kafin cajinta ya ‘kare, kuma zata iya amfani da yanar gizo, sai dai ba komai mutum zai iya yi da ita ba idan akayi la’akari da sabbin wayoyin zamani da mutane kan yi amfani da su wajen shiga dandalin Facebook da Whatsapp.
Yanzu haka dai ana sayar da sabuwar wayar Nokia 3310 akan kudi ‘kasa da Naira dubu 20, wanda ake kyautata tsammanin mutane zasu sayi wayar su yi amfani da ita a matsayin waya ta biyu.
Kamfanin Nokia dai ya yi ta fama wajen kasancewa kafada da kafada da sauran kamfanonin wayoyin zamani, amma hakka bata cimma ruwa ba, daga karshe Microsoft ya saye kamfanin Nokia. Tun daga wannan lokacin Nokia ke yiwa tsofaffin wayoyinsa garambawul yana sayarwa cikiin rahusa.

You may also like