Wayar Samsung ta kama da wuta cikin jirgi


 

An tilastawa fasijoji 75 saukar gaggawa daga cikin jirgin sama bayan da wayar Samsung na wani fasinja ya tarwatse da fidda hayaki.

Samsung Galaxy Note 7 (picture alliance/AP Photo/A. Wong)

Wayar salula kirar Samsung Galaxy Note 7 na daya daga cikin fasinjoji ne ya kama da wuta a cikin jirgin saman, wanda hakan ya ja hankalin hukumomi a filin tashi da saukan jiragen sama na birnin Baltimore na kasar Amirka daukar matakan gaggawa na sauke fasinjoji 75 da ke cikin jirgin sama na Southwest Airlines don gudun aukuwar asarar rayuka bayan da aka gano wayar ta fara fidda hayaki. Babu dai wadanda suka samu rauni sakamakon aukuwar lamarin.

Kamfanin ‘kera wayoyin zamani na Samsung dai na fuskantar kalubale a baya-bayan nan, inda ko a watan Satumban da ya gabata sai da aka tilastawa kamfanin kera wayoyin da ke Korioya ta Kudu da ta janye adadin wayoyin ta sanfurin Note 7 guda miliyon biyu da rabi daga kasuwannin duniya biyo bayan da aka samu wayoyin da rashin ingancin batura da ke haddasa hayaki. kamfanonin jiragen sama da dama sun haramtawa fasinjoji dake da irin wayoyin Samsung kirar Note 7 shiga jiragensu.

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like