Wes Morgan zai ci gaba da zama a Leicester


Kyaftin din Leicester City Wes Morgan ya sanya hannu a sabon kwantaragi da kungiyar wanda zai kare a watan Yunin shekarar 2019.

Dan wasan, mai shekara 32, ya shiga dukkan fafatawar da kungiyar ta yi a kakar wasan da ta wuce, wacce ta kai su ga lashe gasar Premier ta Ingila.

Morgan ya koma Leicester ne daga Nottingham Forest a watan Janairun 2012 kuma ya buga wasan Lig sau 182.

Dan wasan ya shaida wa shafin intanet na kungiyar cewa, “Ci gaba da murza leda a Leicester City shi ne babban burina. Kowa ya san irin rawar da nake takawa a kungiyar.”

Ya kara da cewa, “Daukar kofin Premier da muka yi abu ne da ba zan taba mantawa da shi ba. Don haka yanzu za mu yi bakin kokarinmu domin ganin mun sake lashe kofin, kuma mun dauki kofin Zakarun Turai.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like