
Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan baya na Ingila Harry Maguire, mai shekara 29, da na tsakiyar Scotland Scott McTominay, mai shekara 26, na daga cikin manyan ‘yan wasa shida na Manchester United da sukai fice a wannan kakar wasan. (Mirror)
West Ham na da kwarin gwiwar kashe fam miliyan 80 domin sayo dan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice, da na Newcastle za su koma Arsenal da Chelsea in bayan kamma tattaunawa kan dan wasan mai shekara 24. (Football Insider)
Barcelona, da Atletico Madrid da AC Milan duka su na tuntuba kan mai kai hari na Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 33. (Mail)
Chelsea ta shirya domin takara da kishiyarta Manchester United domin dauko dan wasan Napoli kuma na gaban Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 24. (Mirror)
Atletico Madrid sun shirya domin dauko dan wasan Wolverhampton kuma mai tsaron gidan Wanderers’ Spanish Hugo Bueno, mai shekara 20. (AS via Sport Witness)
Arsenal da Tottenham na daga cikin kungiyoyin da suka nuna sha’awar dan wasan gaba na Sifaniya Ansu Fati, sai dai Bayern Munich na zawarcin dan wasan mai shekara 20. (Mundo Deportivo – in Spanish)
A wani bangaren kuma Gunners, na kokarin dauko dan wasan Leicester City kuma na tsakiyar Belgium Youri Tielemans, mai shekara 25, a kakar wasanni. (Teamtalk)
Watakil Tottenham ta yi amfani da kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da Atletico Madrid domin daukar dan wasan Belgium winger Yannick Carrasco, mai shekara 29, da mai tsaron ragar Slovenia Jan Oblak, mai shekara 30,idan an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa. (Mail)
An bai wa Real Madrid damar dauko dan wasan baya na Portugal Joao Cancelo, mai shekara 28, daga Manchester City, sai dai kulub din na Sifaniya bai aminta da haka ba ganin cewa ‘yan wasansa na yin abin da ya dace. (Fabrizio Romano via Twitter)
Dan wasan tsakiya na Sifaniya Isco mai shekara 30 na jiran wata dama da zai samu nan gaba ta hanyar wani eja daga Everton, a daidai lokacin da ya ke duba komawa wani kulub din, bayan an kawo karshen kwantiraginsa da Sevilla. (TuttoJuve – in Italian)