
Asalin hoton, Getty Images
West Ham ta kulla yarjejeniya dan kwallon Brazil Luizao wanda ta dauko daga kungiyar Sao Paulo.
Dan wasan mai shekaru 20, zai hade da Hammers daga ranar 1 ga watan Janairu idan har ya samu takardun da ake bukata na soma taka leda a Ingila.
Luizao ya amince da kwangilar taka leda har zuwa shekara ta 2026.
Sanarwar da West Ham ta fitar ta ce “Kowa a West Ham na maraba ga Luizao zuwa wannan kulob din kuma muna yi masa fatan alheri.”
A cikin watan Mayu ya soma murza leda a Sao Paulo kuma ya taimaka mata kai wa wasan karshe na kofin Copa Sudamericana.