WHO: Marburg ta sake bazuwa a Ghana | Labarai | DWHukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta tabbatar da samun karin mutum biyu dauke da cutar Marburg a kudancin kasar Ghana. Wani babban jami’in WHO a kasar Ibrahima Soce Fall ne ya sanar wa da ‘yan jarida haka a Larabar nan, makonni biyu bayan da aka fara sanar da bullar cutar mai hatsari kamar na Ebola a kasar. 

Da ma dai akwai mutane biyu da WHO din ta ce cutar ta halaka a yankin Ashanti bayan sun nuna manyan alamun kamuwa da cutar da suka hada da; gudawa da zazzabi mai zafi da kuma amai. 

Masana dai na cewa jemage ne ke yada wa dan Adam wannan ciwo da akan iya baza shi ta hanyar taba ruwan jikin wanda ya kamu da shi.You may also like