Wike ya fadawa Buhari: APC ta mutu a  Rivers ziyararka ba zai farfado da ita ba 


Nyesom Wike,gwamnan jihar Rivers  ya ce jam’iyar APC a jihar ta riga ya ta mutu.

A cewar, Simeon Nwakaudu, mai taimakawa gwamnan kan kafofin yada labarai, Wike ya bayyana haka lokacin da yake mai da martani kan ziyarar da shugaban kasa Muhammad Buhari ya shirya ya kai wa  zuwa jihar.

Buhari  na kan ziyarar jihohi da aka samu  asarar rayuka sakamakon tashin hankula.

An shirya shugaban kasar zai ziyarci jihar Benue a ranar Litinin,  ranar Alhamis kuma ya kai makamanciyar irin wannan ziyarar  jihar Rivers.

Amma Wike ya ce ba a sanar da shi ba shirin shugaban kasar na kai ziyara jihar ta Rivers.

“Ba a fada min shugaban kasa ya na zuwa ba,  da kuma dalilin zuwansa.Yana da yancin ya zo kowace jiha,”Wike ya ce.

  “Wata kila shugaban kasar yana zuwa ne domin ya karawa jam’iyar APC daraja da ta riga ta mutu a jihar Rivers.

“Bayan Annabi Isa (AS) ba mu san wani da ya taba tashin abun da ya mutu ba APC ta mutu a jihar Rivers. Duk iya azumi da addu’ar da zaka yi baza ta tashi ba.”

Gwamnan ya ce kamata ya yi shugaban kasar ya kai ziyara jihohi 36 dake kasarnan tun da fashi da makami da yin garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a kasarnan.

Wike ya ce tun da gwamnatin tarayya ta yi watsi da jihar watakila ziyarar ta Buhari za ta iya zamarwa jihar abin alkhairi a fakaice.

You may also like