
Asalin hoton, Getty Images
Wolves na shirin daukar dan wasan gaban Brazil da Atletico Madrid Matheus Cunha matsayin aro.
Dama an shafe makonni ana tattaunawa tsakanin kungiyar ta Premier League da dan wasan kuma tuni suka cimma yarjejeniyar fatar baki.
Ana shirin yi wa dan wasan gwajin lafiya, kuma yarjejeniyar ta aro ce amma da damar sayen shi a karshe kaka.
Wata majiya ta ce Atletico za ta iya barin Cunha ya bar kungiyar bayan kammala wasannin rukunin zakarun Turai.
Cunha ya buga wa Brazil wasanni takwas, kuma wasa daya tilo ya buga wa Atletico a bana.
Sabon kocin na Wolves Julen Loptegui na kokarin farfado da kungiyar da sabbin yan wasa, wadda ta ci kwallaye takwas kacal daga fara gasar Premier League zuwa yanzu.