
Asalin hoton, BBC Sport
Yan wasan Faransa Kingsley Coman da Aurelian Tchouameni sun fuskanci nuna wariyar launin fata, bayan da suka barar da bugun fenareti a wasan karshe na gasar kofin duniya.
An doke Faransa 4-2 a bugun fenareti a hannun Argentina ranar Lahadi, wanda hakan ke nufin sun gaza kare kofin da suka je dashi.
Golan Argentina Emi Martinez ne ya ture kwallon da Coman ya buga masa, yayin da Tchouameni ya buga ta waje.
Tuni Bayern Munich, kungiyar da Coman ke buga wa wasa ta wallafa sakon nuna goyon baya ga dan wasan nata, inda tace tana goyon bayansa kuma tana nanata cewa ”wariyar bata da wuri a harkar wasanni.”
An rika nuna musu wariyar ne a kafafen sada zumunta, irin abunda ya faru da yan wasan Ingila bakake, Marcus Rashford da Jadon Sancho da kuma Bukayo Saka, bayan da suka barar da bugun fenareti a wasan karshe na Yuro 2020.
Kawo yanzu babu wata sanarwar daga jam’ian tsaro kan wannan batu.