
Asalin hoton, OTHER
Da sanyin safiyar Talata ne jirgin da ke dauke da tawagar yan wasan Argentina, da suka lashe kofin duniya na Qatar 2022, ya sauka babban birnin Kasar wato Buenos Aires.
Dama tun ranar Lahadi da yamma ne dubban daruruwa daga ko’ina a fadin kasar suka isa sanannen dandalin tsakiyar birnin, tare da cika tituna don murna.
Kuma tun ranar Litinin suka fara hallara ofishin hukumar kwallon kafar Argentina inda tawagar za ta sauka.
Kazalika wasu masu murnar sun kasa sun tsare a filin jirgin Boenos Aires suna dakon isowar tawagar.
Gwarzon dan wasan gasar kofin duniyar Lionel Messi ne ya fara fitowa daga jirgin yana daga kofin na zinari, daga nan kuma sai sauran tawagar ta biyo shi.
Asalin hoton, OTHER
Hotunan bidiyo sun nuna yadda yan kasar ke ta murnar yin ido-da-ido da kofin, wanda suka ci karon farko tun 1986 a Mexico.
Tun bayan da kasar ta ci kofin na biyu a lokacin marigayi Diego Maradona, Argentina ba ta taba murnar wani biki ba tare da nuna bambancin siyasa ba irin wannan.
Ana sa ran tawagar za su zagaya babban birnin kasar, don sakawa al’umma da suka nuna goyon bayansu tun daga fara gasar har karshe.