
Asalin hoton, Getty Images
Mazauna Unguwar Gwargwaje da ke birnin Zaria a jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun gamu da wani iftila’i bayan da wutar lantarki mai karfi ta yi sanadiyyar mutuwar mutum goma.
Kazalika lamarin ya jawo ƙonewar gidaje masu yawa ƙurmus.
Mazauna unguwar sun ce lamarin ya auku ne cikin daren Laraba yayin da suke barci bayan da aka mayar da lantarki a yankin.
Wannan lamari ya jefa al’ummar Unguwar Gwargwaje cikin yanayi na damuwa bayan da suka wayi garin Laraba babu wasu cikin matansu da ‘ya’yansu da kuma iyayensu.
Al’amarin dai ya faru ne bayan da aka mayar wa yankin lantarki mai karfin gaske har ta fara narka wayoyin wuta na cikin gidaje yayin da yawancin mazauna unguwar ke barci.
A kokarin da suka yi na kashe nau’rorin da ke amafani da lantarki, wasu mazauna unguwar suka rasa rayukansu, kamar yadda Bala Jibrin, wani mutum wanda ya rasa matarsa ya shaida wa BBC.
“Wutar ta kama duka matana da ƴaƴana, amma ita ɗaya matar tawa ce kawai ta rasu.
“Ina kwance a ɗaki sai babban ɗana ya taso yana buga min ƙofa.
“Ya ce ‘wuta ce, kuma za ta yi ɓarna,’ sai na ce ya samu wani abu ya buge wutar, to ita kuma ihu da hayaniyar da ta ji sai ta taso.
“Har ta fito kuma sai ta koma don cire cajin wayarta, to sai wayar ta faɗo ta kama da wuta, sai kawai wutar ta kama ta, ga shi ƙafarta ba takalmi,” ya ce.
Ya ƙara da cewa sun je asibitin Gambo Sawaba amma ba su samu kowa ba har kwananta ya ƙare.
Wani matashin mai suna Ahmad Abubakar Zubairu ma ya gaya min ya yi sa’a bayan da lantarkin ya kusa halaka shi bayan da wayoyin gidansu suka fara hayaki suna narkewa.
“An kawo wuta wajen ƙarfe 12 da minti 20 na dare. Da yake a lokacin muna tare da su mamanmu sai duk abubuwan wuta suka fara hayaƙi.
“Sai na ga ɗakina ya fara hayaƙi, sai na yi maza na je wajen sauya wutar gidan na cire fuyus, sai na ga wutar ta ƙara ƙarfi.
“Sai na yi ƙoƙarin sauya layin daga na Nepa don ya koma janareto sai wutar ta ja ni sosai. Mamata ma ta zo fitowa wutar ta ɗaga ta ta buga a ƙasa.
Mai magana da yawun kamfanin raba lantarki na Kaduna Electricity wanda Jihar kaduna ke karkashin kulawarsa, Abdulaziz Abdullahi ya yi wa BBC Hausa bayanin yadda suka samu labarin.
“Yau da safe mun samu rahoton cewa na samu katsewar waya a Zaria, kuma nan da nan muka tura ma’aikata don yin bincike su ba mu rahoto.
“Nan ba da daɗewa ba za mu fitar da sakamakon binciken idan Allah ya yarda,” ya ce.
Mun kuma tuntubi rundunar ‘yan sandan Jihar ta Kaduna, sai dai kakakin rundunar ASP Mohammed Jalige ya bukaci mu ba shi lokaci ya kammala binciken abin da ya faru.