Kasar Sin wato China ta cire dokar takaita wa’adin mulki daga kundin tsarin mulkinta haka ya sharewa shugaba Xi Jinping hanya inda zai iya cigaba da zama akan kujerar shugabancin kasar har iya tsawon rayuwarsa.
Wa’adinsa akan mulki zai kare ne a shekarar 2023.
Majalisar dokokin kasar ce ta zartar da wannan hukunci lokacin da ta amince da wasu jerin sauye-sauye da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar.
A cikin kuri’u 2964 da aka kada, 2958 sun amince da sauye-sauyen biyu basu amince ba ya yin da uku suka ki kada kuri’a.
Xi ya fara wa’adin mulkinsa na biyu na tsawon shekaru biyar a cikin watan Oktoban shekarar 2017.