Yaƙin Ukraine: Sojojin Rasha na ja-in-ja kan adadin mace-macen yaƙiRussian soldiers

Asalin hoton, Reuters

Takardun sirrin Amurka da aka kwarmata sun bankaɗa yadda ɓangarorin dakarun tsaron Rasha suka samu rashin jituwa lamarin da ya sa har aka zargi ma’aikatar tsaro da rage yawan mutanen da suka mutu lokacin yaƙi a Yukren.

Rasha dai na ba ta cika yawan magana a bainar jama’a game da yawan mace-macen dakarunta a fagen yaƙi.

Sai dai takardun sirrin sun nuna jami’an tsaron leƙen asirin Rasha FSB na iƙirarin cewa hukumomi ba sa haɗa ƙirge da mace-macen Dakarun Tsaron Ƙasa na Rasha da sojojin haya na Wagner da kuma wasu.

Rasha dai tuni ta yi gargaɗin cewa bayanan da aka kwarmata ɗin mai yiwuwa na jabu ne, kuma da gangan Amurka ta yasar da su.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like