Ya Kamata A Haramta Jam’iyyar PDP –  Gwamna ShatimaGwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana cewa ya kamata a haramta jam’iyyar PDP a Nijeriya inda ya nuna cewa jam’iyyar na da alaka da miyagun al’amurra.
Gwamnan wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ya bayyana haka ne a Makurdi inda ya yi ikirarin cewa idan da PDP ce ta lashe zaben 2015, da a yanzu Nijeriya ta zama tarihi. Shettima ya kuma nuna cewa halin kunci da ake ciki a yau, duk ya samo asali ne daga irin miyagun manufofin PDP ne a shekaru 16 da ta yi kan mulki.

You may also like