Ya kamata Ace Na Kama Shugaba Buhari Lokacin Ina Kan Mulki – Goodluck Jonathan 


 

A Lokacin Da Nake Kan Mulki Buhari Ya Furta Kalaman Da Ya Kamata Na Kama Shi Amma Na Kyale Shi. 
A wani abu mai kama da martani tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana dalilin da ya sa bai kama shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a yayin da yake mulki ba. 
A cewar Jonathan yayin da Buhari ya ke neman takara a shekarar 2015 karkashin Jam’iyyar APC ya taba furta cewa, “Matukar ya ci zabe aka murde masa to za a yi Kare jini Biri jini”.

Wanda kowa ya san wannan furuci ne da zai iya tayar da hankali kamar irin abinda ya faru a 2011 da Buhari ya fadi zabe irin yamutsin da ya biyo baya. Jonathan ya jaddada cewa, da ya so kama Buhari da zai iya kama shi.

You may also like