Ya Kamata Buhari Ya Gayyato Johnathan Domin Ya Koya Masa Yadda Ake Mulki – Dr. Ahmad Gummi



A yayin zantawar sa da manema labarai Dr Ahmad Gummi ya bayyana cewa, dole Buhari ya gayyato Jonathan domin ya nuna masa yadda zai gabatar da mulkinsa. 

Yace ba ya goyon bayan cin hanci, amma yadda Buhari yake yaki da cin hanci bai yi ba.

Ya kuma kara da cewa, Jonathan ya fi Buhari iya mulki, musamman idan aka duba yadda shi Jonathan din ya gina makarantun Almajiri  guda 400 a Najeriya, da an bi wannan tsarin da yanzu an kawar da Boko Haram.
Ya kara kuma da cewar dole Buhari ya saki Nnamdi Kanu, shugaban masu son ganin sai an raba Biyafara da Najeriya, domin a cewarsa hakan zai sa wasu su ji tausayinsa su goyi bayan abinda yake kira akai, ya bayyana cewar dole a zo a zauna da su a basu abinda suke bukata, a tattauna da su ba wai a sanya shi a kurkuku ba. Ya kara kuma da cewar Sambo Dasuki ma ba’a kama shi bisa adalci ba, dole shi ma a sake shi.

You may also like