Ya kamata Buhari ya Sauka daga Kujerar sa –  PDP


Bangaren shugabancin Ahmad Makarfi na jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP, ya nemi da shugaban kasar, Muhammadu Buhari da ya bar kujerarsa bisa zargin gazawa.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, jam’iyyar ta nuna rashin jin dadinta dangane da karayar arzikin da kasar ta samu kanta a ciki.A ranar Laraba ne dai hukumar Kididdigar Kasar ta fitar da wasu alkaluma da ke nuna tattalin arzikin kasar ya samu tawaya da kaso biyu, a watanni ukun da suka gabata.

Jam’iyyar ta PDP ta ce ” mun yi tarayya da sauran ‘yan Najeriya da ke kiran shugaba Buhari da ya bar kujerar shugabancin kasar idan dai har ba zai iya gyara matsalar tattalin arzikin da ya jefa kasar a ciki ba.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like