Ya kamata Buhari ya sauka daga mulki—Abdulmuminu Jibril


abdulmumin-jibrin-2

Dakataccen ɗan majalisar wakilai ta ƙasa Hon. Abdulmuminu Jibrin kofa ya shawarci shugaba Buhari, ya sauka daga mulki idan akayi la’akari da rashin lafiyar da shugaban yake fama da ita. inda yace magoya bayan shugaban na cikin damuwa inda suke ƙorafi da kakkausar murya ba tare da tsoro ba, suka rike fata da kuma addu’a ga shugaban.

Ɗan majalisar wakilan ta  tarayya daga Kano mai wakilatar mazaɓar Ƙiru da Bebeji, ya lura cewa ƙasar na tana tafiya ne kawai da kanta wajen maganin matsalolin da suke damunta, ta yadda abubuwa da dama anbarsu batare da kulawa ba,kai wani abun ma tari idan shugaban ƙasa yayi ya isa yayi maganin matasalar.

A jeri saƙonnin da ya saka a shafinsa na Tweeter jibrin ya shawarci Buhari ya sauka sannan kuma a bawa Aisha Buhari Muƙami a sabuwar gwamnatin da za a kafa.

Ya kuma bayyan ma bambancin ra’ayi kan cewa ƴan Arewa su rungumi ƙaddara na rasa shugabancin ƙasar nan a karo na biyu, inda yace wataƙila  Allah baya farin ciki da irin shugabannin da ake dasu a arewa a ayanzu.

Jibrin yace cuta da mutuwa duk na Allah ne amma duk lokacin da ya kalli hoton shugaban ƙasa to yana ƙara gamsuwa cewa lallai shugaban hutu kawai yake buƙata.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like