Ya Kamata Jama’a Su Dinga Zaɓen Shugabanni Masu Ilimin Addini – Hon Madada


A rana ta goma yayin gabatar da tafsirin watan Ramadan, wanda Ustaz Yakubu Jama’are da Alaramma Shehu Ibrahim Ahmad Keffi suke gabatarwa a Masallacin JIBWIS da ke sabon layi cikin garin keffi, kafin daga bisani Hon. Ahmed Aliyu Wadada Braden Keffi dan takarar Gwamnan jihar Nasarawa shi ma ya karbi Alarammancin domin jan baki ga Malam, lamarin da ya ba kowa mamaki a wajan Tafsirin.

Daga karshe Hon Ahmad Aliyu Wadada ya tunatar da jama’a inda ya fara da suratul Ankabutu daga farkon Aya zuwa Aya ta biyar, ya kuma kawo misalin yadda gizo-gizo yake da kuma yadda yake da gida amman ba ya tare masa ruwa ko iska, wanda hakan yake tamkar misalin wanda ya zabi shugaban da bashi da ilimin Addini ne.

Ya ja hankalin jama’a da su kaunaci zaman lafiya da amfani da abubuwan da suka ji a wajan karatun.

You may also like