Wani dan siyasa a Jihar Katsina, Honourable Zulkifilu Bawa Bawasa ya koka a kan yadda aka bar sauran jam’iyyun da suka hada kai suka samar da jam’iyyar APC kafin zaben shekarar dubu biyu da sha biyar a baya wajen rabon mukamai a jihar.
Zulkifilu Bawasa Jibia ya bayyana wa manema labarai cewa jam’iyyu irin su ANPP da ACN ba su samu mukamai ba kamar yadda ita jam’iyyar CPC ta samu.
Ya bayyana al’amarin a matsayin wanda ka iya kawo rabuwar kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ta APC a zaben shekarar 2019 da ke tafe.
Zulkifilu Bawasa ya yi nuni da bayanin da uwargidan shugaba kasa, Aishatu Buhari ta yi da BBC Hausa a matsayin abin dubawa, domin kamar yadda ya ce zabe abu ne wanda akan yi duk bayan wani lokaci, yana mai cewa, “idan ka guji mutanen da suka mara ma baya a yau to a gobe ba zai yiwu su waiwayo ka ba”. Inda ya kira ga jam’iyyar APC da Shugaba Buhari su dubi al’amarin a dukkanin matakai.
Ya kuma yi tsokaci dangane da rashin karbar mukamai da wasu ‘yan siyasa suka yi a matsayin watsa ma wannan gwamnati mai ci yanzu kasa a idanu, inda ya buga misali da rashin karbar mukamin Jakada Dakta Mainasara Bugaje a matsayin abin dubawa duk da cewa shi Bugajen ya ba da uzurinsa na rashin amincewa da mukamin da aka bashi.
A kan haka ne Zulkiflu Bawasa ya yi kira ga jam’iyyar APC da Shugaba Buhari a kan su dage kafa wajen ganin sun daidaita siyasar kafin lokacin zabe.
Ya kuma ya yaba wa Shugaba Buhari a kan kokarinsa na samar da tsaro a kasar nan tare da kira ga al’ummar Nijeriya da su ci gaba da bashi goyon bayan ganin an samu dawwamammen zaman lafiya a kasar.