Ya Kamata ‘Yan Najeriya Su Martaba Shugaba Buhari – Omotola Jalade


Fitacciyar jarumar finafinan kudun Omotola Jalade Ekehinde ta yi kira ga al’ummar Nijeriya da su marawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya bisa yadda aka san shi a matsayin mutum mai gaskiya a baya.
 

Omotola ta kara da cewa har yanzu akwai  kudurorin da shugaban bai ida cin masu ba don haka sai an kara da hakuri. Kuma tana da yakinin cewa shugaban zai cika alkawurran da ya yi wa al’ummar Nijeriya kasancewar mutum ne mai gaskiya da rikon amana.

You may also like