Sunansa Adamu da safiyar yau ya rataye kansa bayan da abokansa suka tuhume shi da satar waya. Lamarin da ya haifar da rigima a tsakanin su. Marikiyarsa ta shaida wa majiyar Arewa24news cewa Marigayin dan asalin garin Misau ne da yazo neman kudi garin Jimeta a jahar Adamawa.
Marigayin ya aikata aika-aikar aika ruhin sa zuwa kiyama ne a unguwar Bauchi Street dake garin jimeta fadar mulkin jahar Adamawa. A yayin daukar wannan rahoto, jami’an tsaro suna shirin daukar gawar.