YA KASHE MATARSA SABODA BATA BASHI ABINCI AKAN LOKACI 



Rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun cika hannu da wani dan shekaru 50 mai suna Tanko Bamaiyi bisa zarginsa da kashe matarsa mai shekaru talatin a kauyen Maigoge dake karamar hukumar Mariga a jihar Neja saboda ta ki ba shi abinci.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, a ranar da lamarin zai auku, an ga wanda ake zargin suna sa-in-sa da matar tasa akan abinci, inda daga bisani ya dauko adda ya daba mata wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta. Bayan ya sassare ta sai ya jefa addar cikin rafi.

A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi bayan rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da shi, Tanko ya bayyana cewa “a yayin da cacar bakin na mu ya yi nisa, sai na sassare ta da adda wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta. 

“A koda yaushe ba ta ba ni abinci da wuri kuma idan na yi magana sai ta zage ni. Ko ‘yarmu ‘yar shekara goma da muka haifa na tambaya game da abinci sai ta tsoma baki tana zagina. 

“Saidai ina neman gafara domin na yanke hukuncin ne cikin fushi. Sharrin Shaidan ne. Kuma ina fatan surukai na za su yafe min. Na yi nadamar abinda na aikata”. 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Peter Sunday ya bayyana cewa nan bada jimawa ba za a mika wanda ake zargin ga kotu domin yanke masa hukuncin da ya kamata.

You may also like