Wani mai shekaru 24 magoyin bayan kungiyar Chelsea ya mutu bayan ya yanke jiki ya fadi sakamakon nasarar da Barcelona ta yi akan kungiyar a gasar cin kofin Zakarun Turai a daren ranar Larabar da ta gabata.
Lamarin wanda ya auku a kasar Ghana, mamacin mai suna Emmanuel Offin, wanda aka fi sani da Nana Yaw, wanda yake sana’ar sayar da wayoyi, ‘yan uwansa sun bayyana shi a matsayin dan a mutun Chelsea.
Offin ya mutu ne a hanyar kai gida bayan ya yanke jiki ya fadi jim kadan da tashi daga wasan.