Ya zagi Allah,shi ko ya amshi ransa


49160216-cached

 

 

Wani dan jaridar kasar Jordan mai suna Nahid Hattar  wanda ya wallafa wani zanen batanci game da Allah ya rasa ransa a cikin wani yanayi mai ban ta’ajibi.

Nahid ya mutu a lokacin da ake gaf da gurfanar da shi a gaban kotun babban birnin kasar Jordan wato Amman,sakamakon wani mutum da bindige shi har lahira.

A cewa wata sanarwar da maka’aitar tsaro ta kasar Jordan ta fitar,dan jaridan ya rasa ransa duk da kokarin da likitoci suka yi na ganin sun cece shi.

An tabbatar da cewa an kama makashin wanda yanzu haka ake ci gaba da yi masa tambayoyi.

Shugaban kungiyar ‘yan jaridar Jordan Tarık el-Mumini ya ce wannan kisan da ake yi,ya taka dokokin kasa da kasa game hakkin fadar ra’ayinsa.

A ranar 13 ga watan Agustan da ta gabata ce,Marigayin ya wallafa wani zanen batanci game Allah a shafinsa na Facebook.Abinda yasa shugabannin kasar Jordan suka cafke shi domin tisa kewarsa gaban kotu.

You may also like