Ya Zama Wajibi Ga Duk Wanda Zaiyi Aure ayi Masa Gwajin Kanjamau – Gwaman Jigawa


Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da kudurin da ta shigar akan maniyyata aure su yi gwajin kwayar cuta mai karya garkuwar jiki, wato Kanjamau.

Auwal D. Sankara (Fica), Mataimaki na Musamman ga Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa akan Sabbin Kafafen Sadarwa shi ne ya bayyana haka a shafinsa na facebook, a inda ya bayyana cewa; kuduri da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ya tura gaban Majalisar Dokoki kuma suka amince da shi, da ya zama tilas akan masu niyyar aure su yi gwajin cuta mai karya garkuwar jiki (HIV/AIDs) ya fara aiki a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da Gwamnan ya halarci daurin auren Mu’azu Atafi Hadeja da Amina Jibrin.

Wannan kuduri da ya zama doka an yi shi ne domin rage yaɗuwar wannan cuta a Jiha da kuma samun lafiyayyen al’uma.
Ɗaurin Auren wanda aka yi a Babban Masallacin Juma’a na garin Dutse, an ɗaura ne bayan an kawo shaidar lafiyar ma’auratan na cewa basa ɗauke da wannan cuta.

Sauran shaidu da suka halarci daurin auren sun haɗa da Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa Barr. Ibrahim Hassan Hadejia, Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha Hon. Ado Sani Kiri, Galadiman Dutse da sauran mashahuran mutane.

You may also like