Yada Labarin Karya Na Mutuwar Shugaban Kasa Ba Sabon Abu Bane A Nijeriya Don Ko Ni Sau 12 Ina Mutuwa – Obasanjo


 

 

Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yada labarin karya da aka yi a kwanakin baya game da mutuwar shugaba Muhammadu buhari ba wani abu bane sabo domin kuwa shi ma sau 12 yana mutuwa a tsawon wa’adin mulkinsa na shekaru 8 da ya yi tsakanin 1999 zuwa 2007

Obasanjo ya bayyana wadanda suka yada labarin mutuwar shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mutane marasa imani, mayaudara kuma marasa kishi

A wata sanarwa da Obasanjon ya fitar jiya ta bakin mataimakinsa na musamman akan harkokin yada labarai jiya a Abeokuta, tsohon shugaban ya ce “A maimakon yada irin wannan labari da zai haifar da zulumi da dar-dar, kamata ya yi mu yi shugaban kasarmu addu’a ta yadda zai dawo bakin aiki cikin walwala, koshin lafiya da karsashin da zai ciyar da kasarmu gaba

Obasanjo ya ce “Ni kaina an yada jita-jitar mutuwata sau 12 a lokacin ina mulki. Masu irin wannan dabi’a ban san abinda suke amfana daga hakan ba, amma dai ina shawartarsu da su tuba ga ubangiji”

Ana dai sa ran shugaba Muhammadu Buhari da ya tafi hutun kwanaki 10 a kasar Ingila zai dawo gida Nijeriya a makon nan da za mu shiga

You may also like