
Asalin hoton, PA Media
Ƙasashe da dama sun yi bikin tarbar sabuwar shekarar 2023 duk da yake ba a yin bikin a tare saboda lokuta da suka bambanta a ƙasashe.
Kiribati ce ƙasar Pacific da ta fara bikin shigowar sabuwar shekarar, sai New Zealand da ta bi sahu bayan sa’a ɗaya.
Dubban mutane ne suka yi dafifi a Sydney domin kallon wasan wuta mai tartsatsi da dallare sararin samaniya cike da mabambantan launuka.
Asalin hoton, BIANCA DE MARCHI/EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
A Sydney, an harba tartsatsin wuta daga gadar Harbour da Opera House
Asalin hoton, Getty Images
Mutane da dama sun hallara domin kallon wasan wuta a ƙarƙashin bishiyoyi da ke lambun Sydney Botanic Gardens
Asalin hoton, Getty Images
An yi bikin shigowar sabuwar shekara a Christchurch da ke New Zealand ta hanyar sanya waƙoƙi da kuma harba tartsatsi
Asalin hoton, Reuters
Mutane sun yi dandazo domin shigar tsakar dare a Seoul da ke Koriya ta Kudu
Ƙasashen Afirka kamar Najeriya da Kenya da Uganda da Masar su ma sun yi nasu bikin shiga shekarar 2023.
Ga wasu daga cikin ƙayatattun hotunan da suka fito daga ƙasashen.
Asalin hoton, Getty Images
Yadda aka yi wasan wuta a kogin Nilu a Alƙahira da ke Masar
Asalin hoton, Getty Images
A Nairobi, an harba wuta mai tartsatsi daga hasumiyar Old Mutual Tower
Asalin hoton, Getty Images
Dandazon mutane ne suka yi cika domin kallon yadda aka harba wuta domin yin maraba da sabuwar shekara a Kampala da ke Uganda.
Birnin London ma ya yi murnar zuwan sabuwar shekarar inda aka shafe minti 12 ana ta harba wuta mai tartsatsi – abin da Magajin Garin Sadiq Khan ya ce shi ne mafi girma a Turai.
Wannan ne karon farko da mutane suka taru a babban birnin Birtaniyar domin bikin sabuwar shekara tun bayan ɓarkewar annobar korona.
Ga wasu hotuna masu ƙayatarwa da muka tattaro.
Asalin hoton, PA Media