
Asalin hoton, OTHER
Amurka ta zamo ƙasa ta baya-bayan nan da ta ƙaƙaba dokar wajabta yin gwajin korona ga masu fitowa daga China, bayan da ƙasar ta ce za ta buɗe ƙofofinta ga matafiya masu zuwa wasu ƙasashen daga makon gobe.
Tuni ƙasashen Italiya da Japan, da Taiwan da kuma India suka wajabta irin wannan gwaji ga baƙin da za su fito daga China ɗin, sai dai Australia da Birtaniya sun ce ba za su sanya dokar ba.
Bayan shafe shekara uku da rufe iyakokinta, China ta ce za ta bar al’ummarta su ci gaba da zirga-zirga babu shamaki daga ranar takwas ga watan Janairu.
To amma hauhawar mutane sabbin kamuwa da cutar na tsoratar da wasu ƙasashen duniya.
Ana samun mutane 5,000 sabbin kamuwa da cutar a kowace rana, sai dai masu sharhi na cewa ana rage yawan alƙaluman, domin a cewarsu za su iya kaiwa kusan mutum miliyan guda a kowace rana.
Rahotanni sun ce asibitoci sun cika maƙil kuma mutane na shan wahala wajen samun abubuwa na yau da kullum.
Amurka ta ce rashin samun sahihan alƙaluman masu kamuwa da cutar a kullum ne ya sanya ta ƙaƙaba dokar wajabta gwajin korona ga duk wanda zai shiga ƙasar daga China, da Hongkong da kuma yankin Macau.
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
Sai dai a ranar Laraba ma’aikatar harkokin waje na China ta zargi ƙasashen duniya da kambama lamarin.
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne ƙasar ta Sin ta soke matakin killace duk wanda zai shiga ƙasar daga ƙetare.
Kafin nan, duk wanda zai shiga ƙasar duk wanda ya shiga ƙasar ana killace shi a ɗaya daga cibiyoyin da gwamnati ta tanada.
Kafin ɓullar cutar korona, China ta kasance ƙasar da al’ummarta suka fi fita domin zuwa yawon shaƙatawa.
Sai dai yanzu babu tabbas kan yawan mutanen da za su samu damar fita daga ƙasar a lokacin da za a ɗage wannan haramci, saboda ƙarancin zirga-zirgar jirage da kuma ƙarewar wa’adin takardun tafiye-tafiye na al’umma.
Asalin hoton, Reuters
Japan ta ce daga ranar Juma’a dole ne a yi wa duk wani mutumin da ya shigo ƙasar daga China gwajin korona.
Kuma duk wanda aka samu da cutar za a killace na tsawon kimanin mako guda.
Haka nan kuma za ta taƙaita yawan jiragen da za su tafi ko kuma taho daga ƙasar ta China.
Ita kuwa India ta ce dole ne fasinjoji da za su fito daga China da kuma wasu ƙasashen Asiya huɗu su gabatar da shaidar da ke nuna cewa ba su ɗauke da korona.
Taiwan ma ta ce mutanen da za su shogo ƙasarta daga China ta jiragen sama ko na ruwa dole ne su yi gwajin korona daga ranar ɗaya, zuwa 30 ga watan Janairu.
Malaysia ma ta ce ta sanya ƙarin matakan bibiyan masu ɗauke da cutar.
Italiya ta ce wajibi ne waɗanda suka fito daga China su yi gwajin korona kafin shiga ƙasar.
A yau ne kuma kwamitin kiwon lafiya na Tarayyar Turai ke tattaunawa domin ɗaukan mataki na bai-ɗaya kan matsalar cutar koronar ta ƙasar China.
China dai ta ce tana kan shawo kan cutar, to sai dai babu sahihan alƙaluma kasancewar hukumomin ƙasar sun daina buƙatar a kai rahoton kamuwa ko mutuwa sanadiyyar cutar.
Haka nan kuma a ranar Lahadi ne hukumomin ƙasar suka ce za su daina fitar da alƙaluman masu kamuwa da cutar a kowace rana.