
Yayin da kogin Tigris yake bi da Babban Birnin Bagadaza, yana cike da sirruka da dama. Babu wanda ya san adadin gawarwakin da aka jefa ciki. Shekara ashirin bayan mamayar da Amurka ta jagoranta, har yanzu abu ne mai wuya amincewa da yadda ɗaya daga cikin mafi kyawun wayewa, daɗaɗɗen garin Babylon ya faɗa cikin irin wannan bala’i.
A yanzu, duk da irin daidaiton da aka samu, har yanzu ana danganta Iraki da kashe-kashen ramuwar gayya na masu kishin addini da motoci maƙare da bam da ɓullar mayaƙa ƴan Sunni da ƴan Shi’a masu tsattsauran ra’ayin Musulunci. Wasu daga cikin tushen sun samo asali ne a farkon shekarun 2000, lokacin ikon Amurka da ba shi da na biyu.
Matakin kai mamaya
Ƙungiyar ƴan tawaye ta Al-Qaeda ta sha kai wa Amurka hari a ƙasarta da hare-haren 9 ga watan Satumba.
Amurka ta tsara wani ƙawance domin kai mamaya Afghanistan, cibiyar al-Qaeda a 2001.
‘Nasara’ a nan ta sa nan da nan hankalin Amurka ya karkata ga Iraki. Massoud Barzani, tsohon shugaban yankin Kurdistan na Iraki ya ce shi da abokin hamayyarsa dan siyasar Kurdawa sun samu goron gayyata a sirrance domin kai ziyara Washington a Aprilun 2002.
“An ɗauki matakin ne domin hamɓarar da gwamnatin Saddam ko mun yarda da hakan ko a’a, ko suna son shiga ko a’a,” in ji shi.
Barzani ya yi shawarar cewa Washignton ta shirya wani taro ta kuma gayyaci jagororin ɓangaren hamayya na Iraki, gwamnati mai jiran gado da ke shirin karɓar ragama da zarar aka tsige Saddam Hussein. An yi taron a London cikin Disamban 2002 inda aka amince da tsarin tarayya da dimokraɗiyya a Iraki.
Sai dai Barzani ya ce ƙararrawa na ƙara yayin da yake shaida abin da ya bayyana da “sha’awar ɗaukan fansa” da wasu daga ɓangaren Shi’a suka bayyana. A ƙarƙashin Saddam Hussein, an murƙushe akasarin ƴan Shi’a a Iraki.
Daga nan sai Amurka da Birtaniya suka gabatar da batun yaƙi kan dalilai na kasancewar makaman ƙare dangi a Iraki wadanda ba a taɓa gani ba. An ƙaddamar da samamen sojoji ranar 19 ga watan Maris ɗin 2003 inda aka riƙa luguden wuta ta sama kan Bagadaza.
Ƙarshen Saddam
Mako uku bayan nan, ranar 9 ga watan Aprilu, Saddam Hussein ya yi rangadi na ƙarshe a unguwar ƴan Sunni – Adhamiya da ke Bagadaza. Dakarun Amurka tuni sun kutsa cikin birnin kuma ya rage ƴan sa’oi su rusa ɓutum-ɓutumi.
Ɗan jaridar Iraki Diyar al-Omari yana Bagadaza a lokacin. Ya ce ƴan Irakin da suka taru a dandalin ba su iya sauke ɓutum-ɓutumin ba da farko. Lamarin da ya sa sojojin Amurka suka yi amfani da motoci masu sulke.
Sai dai ba su iya kai ɓutum-ɓutumin ƙasa ba gaba ɗaya. Wata alama ce ta abin da ke tafe – gwamnatin Saddam Hussein tana da tasiri sosai a tsakanin al’ummar Iraki da aka gina shekaru masu yawa.
Bayan faɗuwar Bagadaza, shugaban Iraki da iyalinsa sun fice zuwa Lardin Anbar. Ali Hatem Suleiman, wani jagoran ƴan Sunni a Iraki, ya kare matakin Saddam Hussein.
“Anbar ne matattarar ƴan Sunni kuma cibiyar Larabawan Iraki a don haka ya zama waje mai tsaro.”
Ƙawancen Amurka ya yanke shawarar kakkaɓe Jam’iyyar Ba’ath daga al’ummar Iraki – tsame jam’iyyar Saddam Hussin daga siyasa da al’umma. Kasancewa ɗan jam’iyyar ya zama muhimmi wajen samun duk wani irin aiki ko ma ilimi a Iraki. Matakin ya kai ga murƙushe sojojin Iraki da cibiyoyin tsaro da na farar hula.
“Ɓangaren Sunni ne ya fi tafka asara cikin wannan lamarin. An tsame shi an kuma taƙaita matsayinsa,” in ji Ali Hatam Suleiman. “An ɗauke shi a matsayin goyon baya ga gwamnatin Saddam sai dai hakan ba gaskiya bane.”
Hakan ya sa tsoffin sojojin Iraki da jami’an tsaro shiga ƙungiyoyin masu tsatstsauran ra’ayi. Al-Qaeda ta samu wata dama ta sake ɗagawa tare da fara ƙaddamar da hare-hare tswon shekaru.
A hannu guda kuma, sojojin Amurka sun kama Saddam Hussein a Disambar 2003. Shekaru uku bayan nan kuma, aka same shi da laifin cin zarafin bil adama inda kuma aka yanke masa hukuncin kisa.
Zartar da hukuncin kisan a ranar babbar sallah, ɗaya daga cikin ranaku masu muhimmanci a Islama, ya janyo fushin jama’a musamman a sassan Lardunan ƴan Sunni da ke Iraki da kuma wasu ƙasashen Larabawa.
Tsohon Firaministan Iraki Nouri al-Maliki wanda ake kallo yana da kusanci sosai ga Iran ya faɗa wa sashen Larabci na BBC cewa a shirye yake ya nuna ƙarfinsa ko da kuwa ta kasance hakan zai fusakata ƴan Iraki.
“Shi ne jagoran Larabawa ƴan Sunni (Saddam), ta ya ya jagoran Shi’a (Maliki) zai shugabance shi?” in ji al-Maliki.
Al-Maliki ya ce dalilin da ya sa aka hanzarta zartar da hukuncin shi ne gujewa duk wani yunƙuri na ƙalubalantar matakin kotun. Ya yi fargabar za a iya mayar da Saddam Hussein zuwa ƙasar waje daga baya kuma a sake shi.
Lamarin ya ƙara janyo taƙaddama bayan ɓullar bidiyon yadda aka zartar da hukuncin. A bidiyon an ga yadda Saddam Hussein ya kasance cikin nutsuwa abin da ya sha banban da abin da wani babban jami’in tsaron Iraki ya faɗa a lokacin. Ya ce jikin Saddam na karkarwa a lokacin da yake kai kansa ga igiyar.
Adawar ƴan Sunni
Yayin da adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru, a ƙarshe Amurka ta shawo kan ƴan Sunni su shiga yaƙin da ake na fatattakar al-Qaeda inda aka murƙushe ƙungiyar ƴan tawayen. A shekarar 2011, akasarin sojojin Amurka da Birtaniya sun bar Iraki.
Amma adawar da ƴan Sunni suka nuna kan tsare-tsaren Firaminista al-Maliki ta ƙara ruruwa inda matasa maza suka riƙa yin zaman dirshan kusa da Fallujah. Jagoran ƴan Sunni Ali Hatem Suleiman ya bayyana buƙatunsu.
“Ɗaukar mataki kan ƴan Sunni, rashin adalci a shari’a da siyasantar da dokoki da kuma ɓangaren shari’a na Iraki,” in ji shi.
Al-Maliki ya yi fatali da hakan inda ya ce al-Qaeda na fakewa da zaman dirshan ɗin, tana dakon samun wata dama domin sake dawowa. A ƙarshen 2013, al-Maliki ya bai wa sojoji umarnin su yi wa dandalin ƙawanya. Hakan ya sa an samu ƙaruwar rashin daidaito a ciki da wajen iyakokin Iraki.
Al-Qaeda ta sake yin ɓaddakama inda ta sake fitowa da ƙarfinta. Birane da dama sun faɗa hannun abin da aka zo ana kira IS.
Da alama sojojin Iraki sun ɓace. “Sojojin da aka gina cikin shekara 10, sun ɓace a sa’oi 10,” in ji tsohon shugaban Ƙurdawa Massoud Barzani.
Tsohon Firaminista al-Maliki yana mamakin yadda kwamandojin rundunonin sojin suka iya janyewa ƴan sa’oi kafin nausawa IS. Haider al-Abadi ya maye gurbin al-Maliki a matsayin Firaminista kuma ya fi fito da matsalolin.
“Ya kasance wani faɗan ɓangaranci wanda ya zama babbar matsala,” in ji shi. “IS ta zama ta ɓangaranci amma tsarin ƙasar shi ma yana nuna ɓangaranci.”
Sai dai al-Abadi ya ƙi bayyana tsare-tsaren al-Maliki a matsayin na ɓangaranci kuma yana da nasa bayanan kan dalilin da ya sa wasu biranen ƴan Sunni suka yi maraba da IS.
“Akwai cin hanci a tsarin tsaron ƙasar,” in ji shi. “Ƴan Iraki sun rasa ƙwarin gwiwa a kai kuma a shirye suke su ha da kai da sauran domin kare kansa.”
Wani gagarumin yunƙurin jami’an tsaron Iraki sun taimaka wajen murƙushe IS bayan shekara huɗu. Amma yaƙin ya bar baya da ƙura a Lardunan Sunni. An ga hakan a Mosul, birnin ƴan Sunni mafi muhimmanci.
Da alamar tausayi a muryarsa, malamin da ke ɗaya daga cikin daɗaɗɗun masallatan Mosul ya buƙaci a maido da tsarin baya sannan Iraki ta koma hannun wani kamar Saddam Hussein. Ya buƙaci a ɓoye sunansa.
“Ba mu datacewa a kan abin da ke faruwa a ƙasar nan,” kamar yadda ya ce. “Amurka ta ce ta ƴantar da Iraki amma ta miƙa ƙasar ga Iran cikin sauƙi.”
Amma wa ke da iko kan muhawarar malamai a lokacin da ake fafutukar inganta rayuwa. Al’ummar Iraki matasa ne da ba su da aikin yi.
Idan Iraki ta zama ƙasar da ke samun arzikin ƙasar, ku yi tunanin abin da wannan ƙasar mai tarin arzikin albarkatun ƙasa za ta iya cimma.