
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin kasar Gambia ta ce ta dakile wani yunkurin juyin mulki.
An kama sojoji hudu sannan mutum uku da ake zargi da taimaka musu sun tsere, a cewar wata sanarwa da gwamnati ta fitar.
Babu cikakken bayani game da hakikanin abin da ya haddasa yunkurin juyin mulkin na ranar Talata da zummar kifar da gwamnatin Shugaba Adama Barrow, wanda ya yi nasara a zabe karo na biyu a shekarar da ta gabata.
An san Gambia a matsayin kasar da ake kwanciyar hankali inda masu yawon bude ido ke tururuwa cikinta domin kallon namun daji da hutawa a bakin tekuna.
Hankula a kwance suke a Banjul, babban birnin kasar, inda kowa yake gudanar da rayuwarsa kamar yadda aka saba.
Ba a ji karar harbe-harebn bindiga ba, kuma babu wata alama da ke nuna cewa an aike da dakarun da ke biyayya ga gwamnati wurare na musamman domin ba su kariya.
Sai dai sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce an aike da sojoji cikin shirin ko-ta-kwana domin sanya idanu a wasu wurare.
“An shawo kan lamarin baki daya,” in ji sanarwar.