Yadda Aka Gudanar Da Taron Bita Ga Mata Maniyyata Hajjin Bana A Bauchi


TARON-BITA-300x225

Uwargidan Gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar ta shirya taron fadakarwa na wuni biyu ga mata maniyyata zuwa aikin Hajjin bana daga jihar Bauchi. Taron, wanda ya gudana a babban dakin taro na Babban masallacin Jumma’a na Bauchi, ya samu halartar mata maniyyata daga dukkan Kananan Hukumomi 20 na jihar.

Da ta ke gabatar da jawabinta na bude taron, Uwargidan Gwamnan, ta gode wa Allahu (S.W.T) da ya ba ta ikon sake ganin irin wannan rana, wacce ta ce rana ce mai matukar muhimmanci ga rayuwar dukkan matan da Allah ya sa za su ziyarci kasa mai tsarki don sauke farali.

Hajiya Hadiza M. A. Abubakar ta kuma bayyana cewa, tun a bara da Allah ya ba maigidanta mulkin jihar Bauchi, ta fara shirya irin wannan taro ga mata maniyyata zuwa aikin Hajji daga jihar Bauchi, inda ta ce cikin yardar Allah madaukakin Sarki, za ta ci gaba da gudanar da irin wannan taron ga matan a duk iya wa’adin da maigidan nata zai yi yana matsayin Gwamnan jihar.

Daga nan sai ta yi kira ga matan da su natsu su fahimci abin da za a koyar da su. Don a cewarta, aikin Hajji abu ne da ake yinsa da ilimi, ba wai kawai mutum ya biya kudi ya tafi, shi ne abin bukata ba, babban abin da ya dace, wanda kuma shi ne karantarwar addinin musulunci, ya zamo wajibi ga dukkan musulmi ya san yadda ake gudanar da aikin Hajji kafin ya tafi.

Uwargidan Gwamnan ta kuma shawarci maniyyatan da su kasance jakadun jihar Bauchi nagari, da ma Najeriya baki daya a yayin da suke gudanar da ibadarsu ta aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Tun farko cikin jawabinta na maraba, Kwamishiniyar ma’aikatar harkokin mata da kula da al’amuran yara na jihar Bauchi, Hajiya Asabe Hamma ta mika godiyarsu ga Uwargidan Gwamnan, bisa irin gudumawar da ta ke bayarwa na ci gaban matan jihar Bauchi.

Hajiya Asabe Hamma ta bukaci mata maniyyata aikin Hajjin da su su yi addu’o’in fatan alhairi ga jihar Bauchi, da kasa baki daya a yayin da suke gudanar aikin Hajjinsu a kasa mai tsarki.

Da take jawabin godiya, Hajiya Aishatu Musa Shehu Awak ta mika godiyarsu a madadin dukkan matan jihar Bauchi, musamman wadanda Allah ya yi cikin yardarsa za su ziyarci kasa mai tsarki don saurke farali. Sannan ta mika godiyarta ga Uwargidan Gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza M. A. Abubakar, saboda kokarinta na shirya wannan taron bitar don ilimantar da mata game da yadda ake yin aikin Hajji, kamar yadda Manzon Allah ya karantar.

Da dama daga cikin maniyyatan da wakilinmu ya zanta da su, sun nuna farin cikinsu bisa taron bitar da Uwargidan Gwamnan ta ke shirya wa mata maniyyata aikin Hajji a duk shekara, tare da addu’ar fatan Allah (S.W.T) Ya saka mata da aljannar firdausi.

Malaman da suka gabatar da kasidu daban-daban a taron bitar, sun hada da Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, Dk. Ibrahim Adam Disina, Malam Usman Ibrahim Giade, Malam Hassan Shinge, da sauran Malamai.

You may also like