Yadda aka kashe mace mai yawon wa’azi da wadansu mutum uku a Kubwa


14AMI5

 

Al’ummar garin Kubwa da ke yankin Bwari a Birnin Tarayya, Abuja, sun hadu da matsalar kashe-kashen gilla a makon jiya inda cikin kwana uku a kashe mutum hudu a lokuta da wurare daban-daban. Kisan da ya fi daukar hankali tare da yayatawa a kafofin watsa labarai shi ne na wata mai wa’azin Kirista da ke yawo da safe mai suna Deaconess Eunice Elisha wadda aka tsinci gawarta yashe a ranar Asabar da ta gabata a wata mahada da ke kusa da gidansu a unguwar Bazango da ke Kubwada yanka ta a wuyarta da hannu da kafa.
Mijin marigayiyar Fasto Elisha Olawale a zantawarsa da ’yan jarida ciki har da wakilin Aminiya a gidansu, ya ce da farko ya samu labarin aukuwar lamarin ne daga wajen ’ya’yansu biyu da s ka je filin kwallon unguwar da safe. Ya ce yaran sun garzayo gida suka shaida masa cewa “Baba mun ji ana cewa an ga gawar wata mai wa’azi yashe a unguwar nan tare da lasifikanta na hannu. Nan take muka je wurin inda wani dan sanda ya ce an wuce da gawarta babban ofishinsu na Kubwa.
Fasto Elisha ya ce bayan sun isa ofishin, sai ya tabbatar matarsa ce. Ya ce kamar mako guda kafin aukuwar lamarin, matarsa wadda kullum take gudanar da yawon bishara a unguwar tsakanin karfe 5:00 zuwa 6:00 na safe ta shaida masa cewa, wani limamin masallaci a unguwarsu ya dakata daga ci gaba da yin wa’azi a daidai lokacin da ta zo masallacinsa har sai bayan da ta tsaya daga yin nata sannan ya gaya wa jama’arsa cewa abin da matar nan ta fada game da ubangiji, gaskiya ne.
“Na amsa mata da cewa, ni Musulmi ne a da, saboda haka ta yi hattara da abin da limamin ya fada.”
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, ASP Anjuguri Mamzah ya tabbatar da kama mutum shida kan zargin suna da hannu a al’amarin. Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Abuja Alkali Bala ya umarci Mataimakin Kwamishina mai kula da bangaren binciken manyan laifuffuka da leken asiri (CIID) ya jagoranci gudanar da bincike a kan lamarin don gano wadanda suke da hannu a aikata kisan.
A lokacin da wakilinmu ya koma unguwar a ranar Litinin da ta gabata wadansu makwabtan wurin sun ce cikin wadanda aka kama har da wani da ke da shagon kwantena na sayar kayan masarufi a kusa da inda aka tsinci gawar mai suna Abubakar Muhammad da kanensa Nura Muhammad wadanda suka ce an kama su ne a lokacin da suka bude shagonsu da safe a ranar da lamarin ya auku.
Wata majiya ta ce an kuma kama wadansu matasa biyu daya mai sana’ar sanya waka a waya mai suna Nura, daya kuma mai sayar da kati, a wajen da suke gudanar da harkokinsu a unguwar, sai kuma wani da aka kama a lokacin da ya biyo ta wajen inda ’yan sanda suka kira shi suka ce ya shiga motarsu, inji mutanen unguwar. Wata ’yar unguwa ta shaida wa Aminiya cewa ta ji matar tana gudu tana cewa, “Jinin Yesu, jinin Yesu kamar yadda yawanci mutanen unguwar suka ce sun ji, kafin karfinta ya kare ta fadi a wurin.” A wani sako da ya fitar tsohon Shugaban kungiyar Kiristoc ta kasa (CAN), kuma Akibishop na Cocin Katolika na Legas, Anthony Cardinal Okogie, ya gargadi Kiristoci kan yi wa’azi a yankunan da suke da hadari.
Okogie wanda ya aike da ta’aziyya ga iyalan Misis Eunice Elisha da aka a Bazango da ke Kubwa ya gargadi Kiristoci kan su rika amfani da hikima wajen yin wa’azinsu a wuraren da suke ba nasu ba. Okogie ya ce ba zaidauka cewa Musulmi ne suka yi kisan ba, inda ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta samar da cikaken tsaro ga kowane dan Najeriya ba tare da lura da addini ko kabilarsa ba. kuma ya roki Kiristoci su guji daukar fansa, inda ya ce Ubangiji ne Mai daukar fansa.
Kisa na biyu da ya tada hankali a garin na Kubwa ya faru ne a ranar Juma’a da dare inda wadansu dauke da makamai da suka bayyana kansu a matsayin jami’an tsaro suka harbe wani mai suna Malam Maude da ke sayar da katin waya bayan sun auka inda yake kwana a kan wani bene da ke gidan man kusa da mashigar NYSC a babban titin da ya taso daga Abuja zuwa Zuba. Shi dai gidan man wanda ba a amfani da shi na tsawon lokaci, bayanai sun ce akwai kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i da suke amfani da bene da shagunansa a matsayin wurin kwana da ba su gaza 30 ba.
Wani da lamarin ya faru kan idonsa mai suna Abubakar Shagari ya ce mutanen da suka je wurin da misalin karfe 2:00 da farko sun ce musu su jami’an tsaro ne da suka zo yin bincike.

“Sun umarce mu kan mu kwanta daga bisani sai suka bukaci wayoyinmu sai suka binciki aljifanmu suka kwashe mana kudi. Ganin haka sai marigayin ya kalubalanci mutanen inda ya ce idan ku jami’an tsaro ne ai sai ku gaya mana laifin da muka yi tukunna. Daga nan ne ya nemi ya gudu amma suka bi shi kasa suka harbe shi da bindiga sannan suka dau katin waya da yake sayarwa suka tafi.”

Ya ce akwai wani mai suna dangaladima da suka yi wa rauni da bindiga sai wani mai suna Nafi’u da ya fado daga kan bene ya samu rauni. Ya ce daga bisani mutanen sun bi ta wani daji da ke bayan gidan man a matsayin batar da sawu kafin s juya su nufi wata gadar sama da ke kusa da wurin inda wasu motoci biyu ke jiransu, suka sulale, kamar yadda wadansu mutun biyu da suka kwanta cikin dajin suka shaida musu. Ya ce sun sanar da ’yan sanda lamarin inda suka taho suka wuce da mamacin zuwa babban asibitin Kubwa.
Haka ana zargin wadansu matasa da suke kwace wayoyin jama’a da sauran ayyukan fitsara da kashe wani mambansu a ranar Alhamis ta makon jiya a Unguwar Pipe Line, Kubwa inda sakamakon haka ’yan sanda suka rika yin kame a unguwar da ya hada da masu shaguna da ke kusa da sannan aka rusa rumfunan sana’o’i da dama kan zargin ko matasan na boye makamai a cikin tarkace.
Wani shugaban ’yan banga a unguwar ya shaida wa Aminiya cewa bayan ya dawo daga sana’ar acaba da misalin karfe 11:00 na dare a ranar don fara aikin gadi, sai ya ga matasan suna azabtar da dayansu, kuma bayan ya yi bincike ne inji shi, sai suka ce ya sace wayar dayansu ne. Ya ce “Da na kula wahalarwar ta yi yawa sai na bukaci su bar shi haka ko su kai shi ga ’yan sanda amma sai su ka ki. Sai na je karamin ofishin ’yan sanda da ke unguwar na sanar da su, ’yan sandan suka ce za su zo. Kuma saboda ba su zo ba, na sake komawa na sanar da su cewa mutanen nan fa za su kashe shi, sai suka ajiye ni sama da awa daya har motarsu da ta je sintiri ta dawo sannan muka taho, sai gawarsa muka samu su kuma sun gudu. Masu harkoki a wurin duk sun watse sakamakon kame da ake yi sannan beli har da na Naira dubu 50, inji shi.
Sai kuma kisa na hudu ya auku a ranar Asabar din, inda aka ce wadansu matasa da suka yi kaurin suna a harkar daba, a Layin Jaji Street, Kubwa suka kashe wani matashi bayan a lokacin da ya rasto inda suke.

Mai gidan da matashin ke haya ya shaida wa Aminiya cewa matashin wanda aka daba masa wuka a kirji, ya lallaba har kusa da gidan da yake zaune bayan mutanen sun gudu, inda ya fadi kasa ya cika.  Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, ASP Anjuguri Mamzah, ya ce bai samu bayani a kan aukuwar kashe-kashen uku ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like