Yadda aka sako ragowar ƴan matan sakandiren Yawuri da aka sace



.

Asalin hoton, OTHER

Ƙungiyar iyayen daliban makarantar yan mata ta Yawuri da ke jihar Kebbi ta tabbatar da dawowar daliban makarantar biyu da suka rage a hannun ‘yan bindiga.

Ƴan matan na daga cikin dalibai 11 na kwalejin gwamnatin taryya da ake zargin Dogo Giɗe ya yi garkuwa da su, kuma ya sako su ranar Laraba.

Salim Ka’oje, shugaban ƙungiyar iyayen daliban Makarantar Yawuri da aka sace yaransa ne ya tabbatar da isowarsu gida yau Alhamis. Sannan ya ce cikin daliban da aka ceto har da wata daliba da yan bindigar suka yi dauko daga Kaduna.

Ya bayyana wa BBC cewa zuwa yanzu babu wata ɗaliba da ta rage a hannun ƴan bindigar.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like