Yadda Aka Yi Zaben Gwamna A Bauchi




Jama’a maza da mata ne suka yi dandazo don kada kuri’unsu tun da misalin karfe bakwai na safe a yawancin rumfunan zabe, kuma an samar da wadatattun kayan aiki kamar yadda jami’an hukumar suka shaida.

To sai dai wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi Adamu Manu Soro yana sayen kuri’a.

Amma a wata hira da Muryar Amurka Manu Soro ya karyata wannan zargi, ya ce ba shi ne a hoton ba, kuma an yi hakan ne don a bata masa suna amma zai nemi hakkinsa ta bangaren shari’a

A wata sabuwa kuma, gwamnan jihar Bauchi ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wani jirgin sama mai saukar angulu ya yi ta shawagi a karamar hukumarsa ta Alkaleri kuma ba a san dalilin zuwan jirgin ba.

Saurari rahoton Abdulwahab Mohammed:



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like