Yadda ake cinikin takardun kuɗi don kauce wa tsadar rayuwa a Zimbabwe.

Asalin hoton, KB MPOFU

Bayanan hoto,

Noel Ngwenya na musanya takardun kudaden waje da suka lalace kan kashi 50 bisa dari na darajarsu, har ma da sayar da ‘yayan itace

“Kowa na ganin sayar da kaya a kan titina ita ce hanya mafi sauki ta tafiyar da rayuwa, amma dole sai ka zama mai basira.”

Noel Ngwenya, mai shekaru 44, daga gundumar Chivi da ke Lardin Masvingo kan shafe kwanakin aikinsa a tsakiyar Bulawayo, birni na biyu mafi girma a kasar, yana tallata hajarsa ta hanyar yin amfani da lasifika.

Ya kan karbi lalatattu ko yagaggun takardun kudaden kasar waje da manyan shaguna ko wasu ‘yan kasuwa ke kin karba – akasari dalolin Amurka ko kudin rand na Afirka ta Kudu, kudaden da aka amince a yi amfani da su a Zimbabwe.

Mista Ngwenya na biyan abokan huldar kasuwancinsa kashi 50 bisa dari na darajar ko wane irin takardar kudi suka kawo masa – don haka suna samun dalar Amurka daya kan yagaggiyar dalar Amurka 2 ko rand 100 a kan yagaggiyar takardar kudi 200 ta rand.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like