
Asalin hoton, EFCC
EFCC ta ce ta yi nasara a manyan shari’o’i a 2022 mafi yawa a tarihin kafa ta
Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta yi nasara a ƙararraki 2,595 da ta gurfanar da mutane a gaban kotu cikin shekarar 2022.
Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta ce ta samu nasarorin ne mafiya yawa a tarihinta ya zuwa 23 ga watan Satumba.
Hukumar ta bayyana cikin mujallarta da ta fitar bugun Satumba, inda ta ce tana fatan sake samun wasu nasarorin kafin shekarar ta ƙare baki ɗaya.
“Waɗannan nasarori masu abin mamaki sun samu ne a daidai lokacin da yin nasara a kotunan Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, ” a cewar Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa yana mai alƙanta nasarar da ƙoƙarin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a yaƙi da rashawa.
EFCC ta yi nasara a shari’o’in da wasu daga cikinsu sai da suka kai har Kotun Ƙoli da Kotun Ɗaukaka Ƙara, amma akasarinsu an fafata ne a manyan kotunan tarayya da ke faɗin Najeriya.
A ranar Alhamis Abdulrasheed Bawa ya ce hukumarsa ta ƙwato da kuma mayar wa gwamnati naira biliyan 36 a 2022, kuma biliyan 30 sun ƙwace su ne daga hannun tsohon Babban Akanta na Ƙasa Idris Ahmed – wanda ke fuskantar shari’a kan zargin wawure biliyan 109.
Satar kuɗin fansho biliyan 32
A ranar 13 ga watan Afrilun 2022 Kotun Ƙolin Najeriya ta jaddada kama John Yusuf da laifi bayan EFCC ta gurfanar da su tun a Maris ɗin 2012 tare da sauran mutum huɗu.
Hukumar ta tuhume su da aikata laifuka har 16 da suka ƙunshi haɗa baki da kuma satar kuɗin ‘yan fansho da suka kai naira biliyan 32.
Tun farko sai da Babbar Kotun Abuja da ke Gudu ta yanke masa zaman shekara biyu ko kuma biyan tarar N250,000 kan kowane laifi, amma sai EFCC ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli.
Kotun Ƙolin ce maƙura ga John, wanda ya tsere tun 2018 bayan hukuncin kotun da ya ce dole ya yi zaman gidan yari na shekara shida da kuma mayar wa da gwamnatin tarayya naira biliyan 22.9 saboda haɗa bakin da suka yi da sauran wajen sace biliyan 32.7 daga Gidauniyar Fanshon ‘Yan Sanda.
Babban sakatare a Ma’aikatar Ƙwadago
A ranar 5 ga watan Mayun 2022 EFCC ta yi nasara a hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa tsohon Babban Sakatare a Ma’aikatar Kwadago Clement Illoh.
Mai Shari’a Babs Kuewumi na kotun da ke zama a Jihar Legas ya yanke wa Mista Illoh hukuncin zaman gidan yari na shekara 12 bayan kama shi da laifi uku da suka haɗa da karɓar cin hanci da ƙin bayyana kadarori.
EFCC ta zarge shi da ƙin bayyana kadarorin da suka kai naira miliyan 97.3, da kuma karɓar naira miliyan 65 a matsayin cin hanci daga ‘yan kwangilar tsarin kuɗin tallafi da ake kira SURE-P.
Kotun ta yanke masa hukuncin shekara huɗu kan kowane laifi, waɗanda zai yi a tare daga 10 ga watan Oktoban 2019. Alƙalin ya kuma ba da umarnin ƙwace kuɗaɗensa na ƙasashen waje – dala $139,575.50 da fan £10,121.52 – don bai wa gwamnatin tarayya.
Mama Boko Haram
Asalin hoton, Other
A ranar 14 ga watan Yunin 2022, EFCC ta kari hukuncin da Babbar Kotun Jihar Borno ta yi wa Aisha Wakil – wadda aka fi sani da Mama Boko Haram – na zaman shekara biyar a gidan yari.
EFCC ta gurfanar da ita tare da Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shoyode a gaban Mai Shari’a Aisha Kumaliya kuma an yanke musu hukuncin ne ba tare da zaɓin tara ba.
An kama su da laifi biyu da ake tuhume su da su a Satumban 2020. Laifukan su ne haɗa baki da kuma karɓar kuɗi da suka kai naira miliyan N71,400,000 ta hanyar ƙarya.
Janar ɗin boge ya sha ɗauri
Asalin hoton, EFCC
A wata mai kama da haka, EFCC ta samu nasarar ɗaure Bolarinwa Abiodun, wani mutum da yake iƙirarin shi janar ɗin soja ne bayan kama shi da aikata laifi 13.
Kotu ta ɗaure shi shekara bakwai a gidan yari bisa kama shi da laifukan da suka haɗa da karɓar kuɗi ta hanyar zamba, da yin amfani da takardun boge da mallakar takardun da ke ɗauke da bayanan kuɗi na naira miliyan N266, 500,000.
Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo na Kotun Hukunta Laifuka na Musamman da ke Legas ne ya yanke masa hukuncin ranar 7 ga watan Yuli na 2022.
EFCC ta faɗa wa kotun cewa Mista Abiodun ya sha zambatar mutane cewa Shugaba Buhari zai naɗa shi a matsayin Hafsan Sojojin Ƙasa da kuma wakiltar kamfanin Kodef Clearing Resources.
Kotu ta kama shi da laifin amfani da sunan tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da kuma amfani da takardun ƙarya da ya ce Shugaba Buhari ne ya saka musu hannu.
Sauran waɗanda kotu ta ɗaure:
- Francis Atuche: Tsohon Babban Darakta a Bank PHB Plc tare da tsohon Babban Jami’in Kuɗi na bankin Ugo Anyanwu. An ɗaure su shekara takwas a gidan yari
- Sanata Peter Nwaoboshi mai wakiltar Mazaɓar Jihar Delta ta Arewa. An ɗure shi shekara bakwai a gidan yari saboda halasta kuɗin haram
- Tuoyo Omatsuli: Tsohon Babban Darakta a Hukumar Raya Yankin Neja-Delta (NDDC). Da farko wata kotu ta wanke shi kafin daga baya Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umarci a sake yi masa shari’a
- Okey Nwosu: Tsohon Babban Darakta a FinBank Plc, da Dayo Famoroti. An ɗaure su shekara uku saboda laifin zambar naira biliyan 19.2
Dalilan da suka sa muka yi nasara – Bawa
Asalin hoton, Nigeria Senate
“Su ne kyakkyawar niyya, da tsarin doka, da ƙwarewar mutane da aka ɗora wa alhakin aiwatar da su, da kuma tsoron Allah,” in ji Abdulrasheed Bawa.
Lokacin da yake jawabi a wajen wani taro na ƙasa da ƙasa, Bawa ya gode wa Shugaba Buhari sakamakon ƙirƙiro shirin asusun bai-ɗaya na ma’aikatun gwamnati wato Treasury Single Account (TSA) da kuma sanya wa wasu dokoki hannu na yaƙi da rashawa.
“Sanya wa Dokar Hanawa da Kare Halasta Kuɗin Haram ta 2022, da Dokar Daƙile Ta’addanci ta 2022, da Dokar Amfana daga Rashawa ta 2022, matakai ne na shari’a da zimmar daƙile kwararar kuɗaɗen haram,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ba wa EFCC kuɗi dala miliyan 10 don ƙaddamar da sabon sashen yaƙi da halasta kuɗin haram mai suna Special Control Unit against Money Laundering (SCUML).