
Asalin hoton, Getty Images
Kasar Indiya ta taso keyar wasu ‘yan Najeriya kusan dari biyu da sauka hada da maza da mata da kananan yara zuwa gida, sakamakon rashin gamsuwa da yanayin zamansu a kasar ta Indiya.
A maraicen jiya Juma’a ne hukumomin Najeriya suka karbi wadannan mutane a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, wadanda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar, wato NEMA, ta yi dawainiyar kwaso su daga Indiyar.
Bashir Idris Garga, babban jami’in kai dauki na hukumar ta NEMA, ya yi wa BBC karin bayani.
“Akwai wasu ‘yan Najeriya da ke zaune a Indiya, wadanda hukumomin kasar ba su gamsu da zamansu ba, ko kuma sun zama musu damuwa a kasar. Wannan ne yasa suka bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta dawo da su gida.”
Ya ce Najeriya ta dauki matakin kwaso ‘yan Najeriyan su 196 zuwa Abuja.
“Maza ana da 152, sannan mata ana da 44, ciki har da kananan yara su biyar, kuma yawancinsu ba su wuce shekara biyar da haihuwa ba.”
Bashir Garga ya kuma bayyana matakan da aka dauka na binciken lafiyar ‘yan Najeriyan da aka kwaso daga Indiya.
“An binciki lafiyarsu domin a kuma a tabbatar da ba su shigo mana da wasu cututtuka ba. Sauran hukumomi kamar na shige da fice ma sun duba su, sannan a karshe aka ba kowannensu dala 100 ta Amurka domin su yi kudin mota zuwa garuruwansu na asali.”
Sai dai jami’in na NEMA ya tabbatar wa BBC cewa yawancin ‘yan Najeriyan ‘yan asalin jihohin kudancin Najeriya ne, amam akwai wasu kadan cikinsu daga yankin arewacin kasar.
Ya kara da cewa hukumomin kasar Indiya sun koro wadannan ‘yan Najeriyan ne saboda dalilai kamar na takardun zama da suka kare amma ba su sabunta su ba.
Sai dai ya ce har zuwa wannan lokaci, akwai wasu ‘yan Najeriyan da ba a kwaso ba saboda suna da wasu batutuwan da ba su kammala yi ba kamar sauke nauyin wata hidima da gwamnatin Indiya ta yi musu kamar biyan kudaden da aka kashe a kansu, ko biyan wani bashi da ke kansu kafin a bari su koma Najeriya.