Yadda Jami’an Tsaro Na DSS Suka Zakulo Kwamandan ISIS A Jihar Kano Hukumar Tsaro na farin kaya ( DSS)  sun ce sun kama babban kwamandan kungiyar IS reshen yankin Afirka ta yamman wanda ya shirya wata makarkashiya an kai wa Musulmi hari lokacin bukukuwan babbar sallah.

Hukumar binciken farin kaya ta kasar (DSS) ta ce kungiyar masu tada kayar baya ta IS reshen yammacin Afirka (ISWA) ta shirya ta da zaune tsaye lokacin bukukuwan sallah wanda aka yi a makon jiya.

Kungiyar ta shirya kai hare-hare a jihohin Kano da Kaduna da Neja da Bauchi da Yobe da Borno da kuma babban birnin Tarayya Abuja, kamar yadda wata sanarwar da hukumar ta aike wa BBC ta bayyana. Sanarwar ta kara da cewa Husseini Mai-Tangaran wanda shi ne babban kwamandan kungiyar shi ne ya kitsa wani mummunan hari da aka kai a jihar Kano a shekarar 2012.

You may also like