Yadda jami’an tsaro suka tsare Peter Obi a LondonPeter Obi

Asalin hoton, Getty Images

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar LP ya ce jami’ai sun tsare tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi a birnin London.

Mai magana da yawun kwamitin kamfe na jam’iyyar LP, Diran Onifade ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a filin jirgin sama na Heathrow da ke London.

Ta ƙara da cewa jami’an shige da fice na Birtaniya ɗin ne suka titsiye tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like