Shekaru biyu da suka wuce na taba jan hankalin Iyaye Mata, musamman ‘Yan Boko akan wannan gagarumar matsalar da ta kunno wa Mata da’ Yan Matan Musulmai kuma Hausawan mu a wannan rikitaccen Qarni na 21. Amma abin sai qara samun tagomashi yake, musamman daga Matan Alhazai, wanda mafi yawancinsu ma, ba Bokon suka yi ba, kawai dai tsantsar jahilci da kuma wautar giyar kudi ke rudarsu har su ringa ganin hakan a matsayin burgewa da cinyewa ne.
A matsayin ki na Uwa, akwai kufcewar lissafi da rudin qwaqwalwa gami da fuffuka da mashassharar zaucewar HANKALI. Ki dauki ‘Yarki da kike tunqahon tsarki da nasabarta ki kaiwa Dan Daudu ita, wai dan kawai ya zane ta da fulawar Amarci. Ke kina ganin kin yiwa ‘Yarki gata na kwalliyar ke ce raini, ashe ke aka kace, ba masu kallon kwalliyar ba.
Na jima da samun hoton nan tare kuma da son na fadakar da al’ummar Annabi Muhammadu (SAW) irin masifar da wasu ke jefamu. Amma sai na tsagaita dan zurfafa bincike game da yanda wannan harkar take. Ban qasa a gwiwa ba, na nufi sabon gari dake cikin birnin DABO, dan na ganewa yanda al’amura ke gudana a irin masana’antar da ake Qunshin Amare. Da farko da naga gidan bayan da wata Yarinya da muke mutunci da ita ta kwatanta min, nayi matuqar mamaki ace Iyaye ne da kansu ke kawo yaransu wannan guri wai dan kawai a musu Qunshin Amarci.
Bazan boye muku ba, gidan KARUWAI ne (wanda ni dai aka kwatanta min, na je) da kuma ‘Yan Hamsin, wanda su ne masu Qunshin. Gidane da babu shamaki ga duk baqon da yake da buqata. A tsakar gidan akwai qatuwar bishiya wacce a qarqashin ta ake baje harkar Qunshin Amare. Zaman dirshan za kiyi daga ke sai zani iya cinya, a sama kuma iya Qirji, wani lokacin ma akan Dan yaye saman dan a samu damar zane wuyan Amarya da fulawa. Sannan akwai na Manyan Mata da ake shiga Daki da su, saboda su banda PANT ba abin dake jikin su, haka za su zauna Qato yana ta sagaraftu a jikin su da sunan Qunshi.
Na yi dacen samun wata Yarinya ana mata, amma ita ba Amarya ba ce, ‘Yar hannu ce, sai dai nayi imanin batsar da me Qunshin ke yi a duk lokacin da hannun sa yaje jikin ta, tabbas zai iya yiwa ko wace Mace irin wannan batsar. Kun dai san yanda batsa ta zama tamkar shayin Dan Daudu.
Hatta Halwa da Dilka da sai Mace tayi tsirara wani lokacin, a wannan gida Dan Hamsin ne ke yi.
Ya kamata ko wani Uba ya tashi tsaye yasan a wani hali iyalinsa ke ciki yayin da duk ya tashi aurar da ‘Yar sa, dan wallahi Iyaye Mata da dama suna kai yaranku ire-iren gidajen can dan a musu Qunshin Amarci, ba tare da ku kun san me suke qullawa ba. A kunne naji wata Mata na cewa “wallahi mazan ne sunfi matan iyawa, ban da haka me zai sa na kawowa wani Qato ‘Yata”. Kuma ko a dinki ne, haka suke fada, tela namiji yafi tela mace iya dinki. Wanda wannan duk ba komai bane fa ce wayewar DAN DABBA.
Allah ka shiryar da mu akan tafarkin gaskiya, dan Alfarmar Annabi Muhammadu (SAW).