- Ni Abdulmumini Jibril Kofa na samu naira miliyan dari shida da hamsin na gudanarwa a matsayi na na shugaban kwamitin kasafi.
- Kakakin majalisa, Yakubu Dogara ya karbi naira biliyan daya da rabi.
- Mataimakin kakakin majalisa, Yusuf Lasun ya karbi naira miliyan dari takwas.
- Shugaban masu rinjaye na majalisa Femi Gbajabiamila ya karbi Naira bilyan daya da digi biyu.
- Mataimakin Shugaban masu rinjaye na majalisa Buba Jibril ya karbi naira bilyan daya da digo biyu.
- Babban Mai Tsawatarwa Na majalisa Alhassan Ado Doguwa shima ya karbi Naira Biliyan daya da digo Biyu….N1.2b
- Mataimakin mai Tsawatarwa ya karbi Naira Miliyan dari Bakwai…. N700million
- Shugaban marasa rinjaye na majalisa Leo Ogar ya karbi naira biliyan daya da digo biyu.
- Mataimakin shugaban marasa rinjaye Onyema ya kabi naira milyan dari Takwas.
- Mai Tsawatarwa ga marasa rinjaye a majalisa ya karbi naira milyan dari bakwai.
- Mai taimakwa mai tsawatarwa na marasa rinjaye shi ma ya karbi naira milyan dari bakwai.
Ina da dukkan shaidun da ake bukata a wajena wadanda za su tabbatar da wannan ikirarin da na yi akan kaina da kuma shugabanin majalisar tarayya karkashin jagorancin Dogara”, Inji Honarabul Abdulmumini Jibrin Kofa.