
Asalin hoton, MICHELLE COLLINS
Michelle Collins ta ce a kullum tana tsoron shiga ɗakin girkinta da safe, saboda wasu kuregu da suka addabe ta a gidan tsawon sama da shekara uku.
Ba su da aiki sai zilliya da wasan ɓuya, sun rika cinye mata kofar shiga ɗakin girki, kuma sun tattaune katakon da aka yi adon ɗakin da su, sannan suna cinye mata abincin karnukanta.
Matar mai shekara 39, da ke da wurin motsa jiki, ta ce kuregun sun shiga ɗakin ne da daddare, abin da ya sa ko yaushe take riƙe da sandar duka.
Michelle, ta ce “Ban taɓa zaton kuregu za su yi wa gidana haka ba, ba za ka taɓa yarda da abin da suka yi ba, idan ka gani.
“Na yi duk wani ƙoƙari amma abin ya ci tura. Sun birkita min tunani.
“A tsorace nake duk lokacin da zan shiga ɗakin girkina da safe.
Asalin hoton, BBC/TONY JOLLIFFE
Michelle ta shaida wa BBC Scotland cewa ta san matsalar gidanta lokacin da ta fara jin motsi a cikin katanga, sai ta fara ganin tiƙar takardu a bakin ƙofa.
“Ina zaune kusa da bishiyoyin katako, sai su riƙa tsalle suna hawa motoci, ta haka har sai da suka samu damar shiga gidana,” in ji ta.
“Sun haƙa wani dogon rami a ɗakin ajiye shirgi da ke waje, kuma ta nan suke shiga cikin katangar gidan.”
Tana ajiye abincin karnukanta a wani ɗakin kaya, da ke kusa da ɗakin girki – sun riƙa shiga ta bango suna cinye abincin.
“Yanzu can nesa nake ajiye abincin idan zan kwanta, amma idan na tashi da safe sai na ga sun janye zanin da na toshe ramin da suka yi, shi ma sun tattauna shi.”
Ta ce masu kama dabbobi sun yi iya ƙoƙarinsu sun gaji ba su iya kama kuregen ba.
Asalin hoton, MICHELLE COLLINS
Mai kula da kama dabbobi da ke lura da yankin Edinburgh, ya ce ya ga irin tashin hankalin da kuregen suke haifarwa.
“Mafi munin da na gani shi ne wata mata da ke zaune a Fife, sai da suka cinye mata duk wata wayar wuta da ke gidanta, ƙarshe sai da ta sake wayoyin gidan baki ɗaya, hakan ya laƙume kuɗi sama da fan dubu talatin.
“Dayan shi ne wata mata da ita ma ke zaune a Edinburgh da sai da suka lalata wayoyin gidanta, ta jikin katakon sama suka riƙa shiga har ɗakin barcinta.
“Za su iya lalata gida baki ɗayansa.”
Dabarar da yake amfani da ita, ta tsorata kuregen ce su fita daga gidan sannan ya toshe duka ramukan da suka yi.
Amma a wannan karon ya ce kurege uku maza sai da suka kai masa hari lokacin da ya rutsa su a cikin saman gidan.
“Ni duk lokacin da na ke yunkurin kama su guduwa suke yi, amma waɗannan tsalle suka yi suka hau jikina suna yunƙurin cizo na.”
Asalin hoton, MICHELLE COLLINS
BBC Scotland ta tattauna da mutane da dama da kurege suke damu a gidansu da matsalolin da suka haifar musu.
Jacqueline Hewitt, mai shekara 49, da ke zaune a unguwar Gracemount a Edinburgh ta ce masu fitar da dabbobi daga gida sun je gidanta, amma har yanzu tana jin motsi sosai a saman ginin gidanta.
“Ya zuba guba da ta kai kwana tara, kuma duka suka cinye cikin mako biyu da muka zo muka sake dubawa.
“Ya shaida mana kurege abu ne mai matuƙar haɗari, dole mu bi a hankali. Bai damu da ya duba cikin rufin gidana ba.
“Ba mu san inda ramunsu yake ba shi yasa muka kasa rufewa.
“Yata ba ta iya barci saboda saboda sun shiga ɗakin ta da take kwana, kuma zaton da take yi ta saman gini take shiga. Ƙarar motsinsu babu ɗaɗin ji.”
Layne Costello, da ke zaune a kudancin Edinburgh, ta ce tana da fuskantar matsala da kurege tun bayan komawarta gidan shekarar da ta gabata.
Ta ce: “sun riƙa rarake saman ginin gidan da nake da fitulun da suke wurin, lokacin da aka fara ruwa gabanin Kirsimeti sai naga saman na yoyo.”
Asalin hoton, MICHELLE COLLINS
Nan Dickson mai shekara 75, da mijinta Gerry mai shekara 85, suna zaune a yankin Mortonhall na Edinburgh sama da shekara 43.
Nan ta ce: “Karon farko da muka fara samun kurege a gidanmu sun tayar mana da hankali, kukansu ba shi da daɗi. Suna lalata mana kaya, in kuma dare ya yi abin ya fi zama tashin hankali.
“Lokacin da miji ya hau sama domin duba meke damunmu, sai suka hare shi.
“Mun mautuƙar kaɗuwa da ramin da muka ga sun yi a sama.”