Yadda Maryam Sanda Ta Kashe Mijinta Bilyaminu – Labari Daga Bakin Abokin Bilyaminu Wani abokin marigayi Bilyamin Muhammad Bello, wanda ya gamu da ajalinsa a hannun matarsa Maryam Sanda a daren Asabar 18 ga watan Nuwamba, Habib Gajam ya bayyana yadda lamarin ya auku.

Jaridar Inside Arewa ta ruwaito Gajam yana fadin cewa bai taba ganin tashin hankali a rayuwarsa ba tare da rashin kunya irin wanda ya gani a kisan Bilyaminu.

Gajam ya ce, rikicin ya samo asali ne da misalin karfe 9 zuwa 10 na daren Asabar, a gidan ma’auratan, inda Maryam ta bukaci Bilyamin ya sake ta, idan ba haka kuma zata yanke masa mazakuta, wanda hakan ya sa abokinsa Ibrahim Aliero shiga tsakaninsu har sau hudu, a lokacin da Maryam tayi yunkurin caka masa wuka.
Ganin yadda lamarin ke neman yin kamari,  hakan ya sa Ibrahim Aliero kiran wani kawun Maryam, mai suna Auta, sa’annan ya kira wani dan uwan Bilyamin, mai suna Abba, don su zo su shiga tsakanin ma’auratan.

Ana cikin zaman jiransu, sai Maryam ta fasa kwalbar gyada, ta taso ma Bilyamin za ta kashe shi da kwalbar, amma sai Bilyamin ya rike hannuwanta, har ya ji ciwo a hannusa, sa’annan kuma ta cije shi a yantsan hannu.

Ba da dadewa ba sai kawunta Auta ya iso gidan, inda ya ja hankalinsu, tare da yi musu nasiha, nan take dukkaninsu suka amince masa da za su zauna lafiya, daga nan ya yi tafiyarsa, inda shi ma Ibrahim ya raka Bilyamin zuwa wani shagon magani, aka duba masa hannunsa da Maryam ta cije shi, sa’annan suka garzaya ATM ya cira kudi, don biyan kudin gyaran motar matar tasa.

Sai da misalin karfe 11 na dare suka koma gida, inda Ibrahim ya cigaba da zama da ma’auratan har zuwa karfe 12 na dare, yana basu hakuri tare da tausan su, daga nan ya tashi ya nufi gida.

Kwatsam da misalin karfe 2 na ranar Lahadi, sai aka gayyace su zuwa asibitin Maitama, inda Bilya ke kwance rai kwakai mutu kwakai, jini ta ko’ina, ga saran wuka a kirjinsa, kafada, cinya, da shaidan hakori a cikinsa.

Gajam ya ce, Maryam ta amsa laifinta a Asibiti, amma da aka je Caji Ofis sai labari ya sha bam bam, inda yace Maryam tace ita ba ita ta kashe Bilyamin ba, a sanadiyyar fadar da suka yi ne ya yanke da tukunyar shisha, wanda hakan ne yayi sanadiyyan mutuwarsa.

Da aka je gidan su, inda lamarin ya auku, kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda ya umarta, sai aka tarar da dakin a share tsaf tsaf, ta wanke jinin da ya zuba, ta yar da makamin da ta yi amfani da su, sa’annan ta fasa tukunyar shishan da tukunyar fulawar dake dakin.

A yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.

You may also like